An soma bukuwan murnar shiga sabuwar ne tun daren Talata musamman mayan biranen manyan kasashen duniya.
Jihar Kano ta shiga jerin biranen da suka yi bikin murnar shiga sabuwar shekarar 2025, a inda aka gudanar da wani gagarimin taro a filin Mahaha a daren Talata.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya samu wakilcin Mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalama a taron gangamin da daruruwan matasa suka halarta.
An kuma gudanar da jawabai da kuma wasan wuta bayan ga wake wake da a filin.
A kofar gidan gwamnatin kuma matasa sun yi dandazo da cigaba da gudanar da wasa da motoci da kuma babura na kawa, tsawon daren na Talata
Sai dai yayin da ake wannan shagali, wasu kuma na masalatai da coci-coci suna gudanar da addu’oi.
Tuni dai gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba a matsayin hutu shiga sabuwar shekara.