
Tsoffin Mambobin jam’iyyar CPC da suka hade da suka kafa APC sun Jaddada goyon bayansu ga Tinubu.
Tsoffin mambobin jam’iyyar CPC sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC.
Haka na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Tanko Al-Makura ya fitar a inda suka nesanta kansu da rahotannin cewa suna shirin ficewa daga jam’iyyar APC da suka kafa.
Sun bayyana rahotannin ficewarsu a matsayin jita-jita maras tushe, tare da jaddada cewa suna nan daram a cikin APC.
Sanarwar ta samu goyon bayan jiga-jigai da suka haɗa da Aminu Bello Masari da Mallam Adamu Adamu, Sanata Ibrahim Musa da Honorabul Farouk Adamu Aliyu da sauran wasu.
Duk da haka, sun yi kira da shugabancin APC da ya shigar da kowa a tafiyar jam’iyyar a kowane mataki domin samun nasara a babban zabe mai zuwa.