
Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce yara miliyan ɗaya da dubu ɗari uku, ƴan ƙasa da shekara biyar masu fama da ƙarancin abinci mai gina jiki ne ke fuskantar barazanar daina samun tallafi a ƙasashen Habasha da Najeriya.
UNICEF ya ce nan da watanni biyu abinci mai gina jiki da sauran magungunan da yake amfani da su wajen yaƙi da lalurar a ƙasashen biyu za su ƙare saboda rashin masu ɗaukar nauyi.
Lamarin na da alaƙa da matakin shugaban Amurka, Donald Trump na rage tallafin da Amurkan ke bai wa ƙasashen waje.
Mataimakiyar shugabar Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, Kitty Van der Heijden (Hayden), a yayin wani taron manema labarai a jiya Juma’a, ta ce katsewar masu ɗaukar nauyin ayyukan nasu zata mayar da hannun agogo baya a kan nasarorin da UNICEF ya samu wajen yaƙi da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki a cikin sheakaru 25.

A watan Janairun bana shugaba Trump na Amurka ya dakatar da ayyukan hukumar USAID mai bayar da tallafi ga ƙasashen duniya, a wani mataki na rage kuɗaɗen da ƙasar ke kashewa wajen ayyukan tallafi.
Matakin wanda Majalisar Dinkin Duniya da sauran hukumomi da ƙungiyoyi suka yi allawadai da shi, ya jefa fargaba a tsakanin ƙasashe masu tasowa, musamman a nahiyar Afirka, inda ake dogaro da irin ayyukan da USAID ke gudanarwa wajen aiwatar da muhimman abubuwan ci gaba.
USAID ta kasance kan gaba wajen gudanar da ayyukan tallafi a Afirka, inda ta shafe fiye da shekara 30 tana ɗaukar nauyin shiryen-shiryen yaƙi da cutukan da suka addabi jama’a, kamar zazzaɓin cizon sauro da HIV/AIDS da tarin fuka da dai sauran su