
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bude masallacin juma’a a garin Agalawa da ke karamar hukumar Garun Malam.
Limamin masallacin Juma’a na Alfurqan, Dr. Bashir Aliyu Umar, ne ya jagoranci bude masallacin wanda Ahmad Sale Mai Gwanjo ya gina a cikin garin na Agalawa.
A hudubar da ya gabatar, Bashir Aliyu Umar ya bayyana falalar gina masallaci da raya shi, inda ya ce yana daga cikin ayyukan da ladansu baya yankewa har zuwa tashin alkiyama.
Ya yi kira ga mawadata da su yi amfani da dukiyar da Allah ya ba su wajen gudanar da ayyukan da za su amfane su har bayan rayuwarsu.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya sakawa wanda ya gina masallacin da alkairi ya sa ladan a mizanin ayyukansa na alkhairi.
Limaman da aka nada domin ci gaba da jagorantar sallar Juma’a a masallacin sun hada da Musa Iliyasu a matsayin babban limami da kuma Lamin Iliyasu a matsayin na’ibinsa.
Taron bude masallacin ya samu halartar mataimakin gwamnan Kano. Comred Aminu Abdussalam Gwarzo da kwamishinoni da masu bai wa gwamna shawara da sauran mukarraban gwamnati.