Gwamnatin sojin Burkina Faso ta musanta Labarin RFI da ke tabbatar da yadda sojojin ƙasar suka kashe fararen hula a ƙauyukan Dori da Gorgadji.
A cikin sanarwar da ministan tsaron ƙasar ya fitar, ya bayyana labarin da tabbatace ne a matsayin na ƙarya da aka ƙirƙire shi don ɓata sunan ƙasar.
Tun farko sashen Faransanci na RFI ne ya wallafa wani labari da ke tabbatar da yadda sojojin ƙasar suka hallaka fararen hula da ke aikin samar da tsaro a yankunan Dori da Gorgadji, a tsakanin garuruwan Tafagou da Nobiol.
Kafin wallafa labarin sai da RFI ta sami cikakkun hujjoji da suka haɗar da jawabai daga bakin iyalan waɗanda aka kashe, Faya-fayan bidiyo da kuma hotuna.
A cikin jawabin ƙaryata labarin da ministan ya yi, ya buƙaci jama’ar ƙasar da su riƙa kaucewa labaran da ke ƙunshe da farfaganda da ke nufin rarraba kawunan jama’ar ƙasar.
Minista Céletin Simporé ya tabbatarwa da ƴan ƙasar ƙokarin da gwamnati ke yi na tabbatar da tsaro da kuma mutunta ƴancin ɗan Adam.
Gwamnatin ta fitar da wannan martani ne bayan sa’oi 10 da wallafa labarin a manyan shafukan sassan RFI.
