Kamal Umar Kurna
Gwamnatin Kano ta ce ta biya kimanin naira biliyan 2 domin karbo takardar shaidar kammala karatun daliban da gwamnatocin baya suka tura yin karatun lafiya a kasar Cyprus.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan, lokacin da yake bada shaidar karatun ga dalibai 10 daga cikin wadanda aka tura karatun kuma sai yanzu sakamakon su ya iso Kano.
A cewar gwamna Abba abin takaici ne yadda gwamnatin data gabata tayi biris da lamuran daliban duk kuwa da irin alfanun da zasu yiwa al’ummar Kano, gwamnan ya kuma yiwa matasan 10 albishirin basu aikin gwamnati da zarar sun gama bautar kasa.
Gwamna Yusif ya kuma roki matasan dasu girmama wahalar da iyayen su da gwamnati suka yi dasu ta hanyar zaunawa a Kano domin tallafawa al’umma ba tare da sun gudu wata kasar ba.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na cewa daliban 10 sune cikon wadanda a shekarar bara gwamnatin Kano ta basu takardar shaidar karatun su na lafiya tare da daukar su aiki nan take.
