Asibitn Dantsinke dake karamar hukumar Tarauni ya kaddamar da shirin Shayi kyauta ga yara fiye da 140.
Kaddamarwar ya gudana ne a asibitin Dantsinke da ke cikin mazabar Darmanawa, a Karamar Hukumar Tarauni a ranar ….
Shugabar asibitin Hajiya Zinatu Umar Rabiu ce ta kirkiri shirin a karkashin wata gidauniya domin tallafawa al’ummar yankin, musanman marasa karfi.
Shugaban karamar hukumar Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure ya jinjinna wa shugabar asibitin bisa wannan namijin kokari.
“Na yi murna matuka da wannan shari, kuma na yi alkawarin bayar da duk wani hadin kai da goyen baya domin ta cigaba da bunkasa asibitin na Dantsinke dake mazabar Darmanawa a yankin karamar hukumar Tarauni”. In ji shi.
Shugaban sashin kula lafiya na karamar hukumar, Alhaji Muktar Datti Gwarzo ta hannun shugaban kula da harkokin zazzabin Maleria na yankin Yusif Adam ya ce, wannan shine karo na farko da karamar hukumar Tarauni da ta fara gudanar da shayin na yara da kudin Aljihunta kyauta domin ta tallafawa Alummar datake aiki a asibitin datake aikin.
Ita kuwa shugabar Asibitin, bayyana manufar wannan aiki da ta yi da cewa zai rage wa iyaye nauyin kudin kiwon lafiya da tabbatar da an yi wa yaran shayi cikin tsari na lafiya da kulawa ta musamman.
A hirarasu da wakilinmu a yayin taron , Iyayen yaran da aka yiwa shayin sun bayyna jin dadinsu da muhimman ayyukan jin kai da shugaban karamar hukumar ke gudanarwa domin tallafawa al’umma, musamman iyalai masu ƙaramin karfi.
