
Shirye-shiryen sun yi nisa na bikin binne gawar shugaban darikar Katoloka ta duniya Fafaroma Francis a a fadar Vatika.
A wata sanarawa daga fadar ta ce, za a binne shi ne a ranar Asabar.
A wani lamari da ya saba da al’adar da ta shafe shekaru da dama, Fafaroma Francis ya bar wasiyyar da ke bayyana cikakken burinsa na yadda ya ke so a gudanar da binne shi bayan rasuwa.
Fafaroma Francis ya bukaci a binne shi ne a cikin a akwati guda daya a maimakon akwatuna uku da ake binne wadanda suka gaje shi, kuma a cocin Basilica of Saint Mary Major da ke birnin Roma, maimakon Basilica na St. Peter da ke cikin Vatican, wanda yawancin Fafaroma da suka gabace shi ke samun makoma a ciki.
A cikin wasiyyar, ya kuma yi cikakken bayani cewa ba ya son a yi wa kabarinsa kowanne irin ado, yana mai jaddada sauki da kwarjinin da ya yi kaurin suna da shi tun kafin ya hau karagar mulki a matsayin jagoran darikar Katolika.
Fafaroma Francis ya kuma bukaci a rubuta sunansa a harshen Latin — Franciscus — kawai a kan kabarinsa, ba tare da wani karin bayani ko girmamawa na musamman ba.
A sanarwar da fadar Vatican ta fitar, an tabbatar da cewa bugun zuciya da mummunan ciwon zuciya ne suka yi sanadiyyar rasuwar Fafaroma Francis.
Bayanai sun nuna cewa tun da dadewa ya kasance yana fama da matsalolin lafiya da suka hada da lalurar hanyar shaƙar iska, wanda cutar lumoniya ta janyo masa sakamakon bakteriya, tare da hawan jini da kuma ciwon siga nau’i na biyu.
Rasuwar Fafaroma Francis, wanda ya kasance daya daga cikin fitattun shugabannin addini masu saukin kai da kishin talakawa, na zuwa ne tare da tunani mai zurfi daga mabiyansa da sauran al’ummar duniya.
Amsar bukatunsa na wasiyya na iya zama wani sabon salo ga makomar shugabannin addinin Katolika a nan gaba.