Daga Mukhtar Yahya Usman
A ranar Asabar da ta gabata ne tsohon Ministan Tsare-tsare da na kudi kuma ɗaya daga cikin fitattun masana tattalin arziki a Najeriya, Dr. Shamsuddeen Usman, ya gabatar da sabon littafinsa mai taken Public Policy and Agent Interest: Perspectives from the Emerging World ga al’ummar Kano, a wani babban biki da aka gudanar a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).
Ko da yake an kaddamar da littafin a Abuja watanni da suka wuce, Dr. Usman ya zabi birnin Kano — inda ya taso kuma ya fara aikin hidimar jama’a — a matsayin matakin farko na gabatar da shi a Arewacin Najeriya.
Taron ya samu halartar manyan baki da suka haɗa da malamai, sarakunan gargajiya, ɗalibai da kwararru a fannin cigaban kasa.
“Wannan ba kawai gabatar da littafi ba ne,” in ji shi a jawabin sa na musamman. “Hanyata ce ta komawa gida ba tare da kyaututtuka kawai ba — sai dai da ra’ayoyi da za su amfanar da jama’a.”
Daga gogewar duniya zuwa bukatar daukar mataki a gida
Dr. Usman, wanda ya taso a unguwar Garangamawa ta Kano kuma ya yi aiki a manyan cibiyoyin duniya kamar Bankin Duniya da IMF, ya bayyana dalilin da ke haddasa durkushewar Najeriya da gazawar shugabanni wajen kiyaye amanar da jama’a suka ba su.
Ya yi bayani kan matsalar wakilci (principal-agent problem), inda ya ce masu mulki — waɗanda ke matsayin wakilai — sun daina wakiltar talaka sai dai kansu, abin da ya haifar da yanke kauna da rashin amana daga wajen jama’a.
“Wannan littafin yana magana ne akan karyewar alƙawarin dake tsakanin gwamnati da jama’a — wato rashin rikon amana, kamar yadda muke cewa a Hausa.”
Tunani na kaina Kan halin da KASA ke ciki
Dr. Usman ya tuna irin gwagwarmayar da suka yi a matsayinsa na Ministan Kudi da Tsare-tsare domin kafa Asusun Arzikin Najeriya (Sovereign Wealth Fund), wanda aka yi niyyar adana arzikin man fetur ga makomar ƙasa, amma wasu ‘yan siyasa suka bijire masa saboda son rai.
“Wannan ya wuce tattalin arziki kadai — yana magana ne akan dabi’u: tsakanin amfanin kasa da amfanin kai.”
Ya ce wannan rikici tsakanin manufar gwamnati da muradun siyasa shi ne jigon littafin, kuma babban dalili ne da ke hana Najeriya ci gaba.
Tasirin kuskuren kasa kan al’umma
Ya jaddada cewa matsalar ba ta tsaya a cikin littafi ba — tana da tasiri kai tsaye musamman a jihar Kano da yankin Arewa gaba ɗaya.
Ya tabo matsalolin kamar yawan yara da ba sa zuwa makaranta, tabarbarewar ababen more rayuwa, da kuma yaduwar rashin amana a tsakanin matasa.
“Idan matasanmu sun ga cewa na kusa da gwamnati ne kawai ke cin gajiyar kasa, to ba za su yarda da ƙoƙari ko gaskiya ba.”
Ya ce hakan na haifar da matasa marasa makona, marasa kuzari, kuma marasa bangon kwanciyar hankali.
Sabuwar dabarar raya kasa:Jama’a su farka su nemi na kansu
Duk da zafin gaskiyar da ya fitar, Dr. Usman ya mai da hankali kan mafita.
Littafin, wanda aka haɗa shi tare da fitattun marubuta ciki har da Dr. Yemi Kale da Mai Martaba Muhammadu Sanusi II, ya gabatar da tsare-tsare guda huɗu domin sake gyara dangantaka tsakanin shugabanni da jama’a:
- Neman gaskiya da bayyananniyar gwamnati – Talakawa su rika tambaya kuma su sami dama ga bayanai da kasafin kudi.
- Tsayawa kan gaskiya – Jama’a su goyi bayan shugabannin kirki, su kuma fuskanci waɗanda ke cin zarafi.
- Sake gina yarjejeniyar zamantakewa – Talakawa su bi doka su kuma nemi hakkinsu.
- Shiga cikin al’amuran kasa – Kowa ya zama mai faɗa a ji, ko da da zuciya, ko da da baki, ko da da hannu.
Ya rufe da faɗin wani Hadisin Manzon Allah (SAW):
“Duk wanda ya ga mummunan abu, to ya gyara shi da hannunsa. Idan ba zai iya ba, to ya faɗi. Idan ba zai iya ba, to ya ƙi shi da zuciyarsa — wannan shi ne mafi raunin imani.”
Tubalin ci gaban gobe
A yayin taron, aka kuma bayyana kafa Gidauniyar Shamsuddeen Usman Foundation, wacce ’ya’yansa suka kirkiro, domin tallafa wa harkar ilimi, lafiya da fasahar zamani.
“Ba wai zargi kawai muke ba — muna so mu gina makoma. Wannan gidauniya ce hanyar bada gudunmawa domin yara su samu makomar da ta fi namu.”
Fiye da Littafi — Kira ne ga Aiki
Dr. Usman ya rufe da cewa wannan littafi ba na jami’a kadai ba ne, littafi ne da ke kokarin farkar da jama’a domin su fahimci ikon da ke hannunsu.
“Wannan littafi naku ne. Jagora ne don neman cancanta da mutunci a cikin mulki. Mu tashi mu gyara wannan alƙawari da aka karya.”
Yayinda da dakin taron BUK ya dauki sowa da tafi, sako ya bayyana fili: Makomar Najeriya ba za ta dogara da wakilai kadai ba — sai da talakawan da su ne asalin masu mallakar kasa.
