Wasu da ake zargin mahara ne sun afka wa karamar hukumar Bokkos dake jihar Filato, inda suka hallaka mutum biyu tare da ƙona gidaje da kuma coci-coci.
An kai harin ne da tsakar dare ɗauke da manyan makamai waɗanda suka zarta na ƙungiyar ƴan sintiri da ke yankin.
Fudang ya ce maharan sun kuma lalata gonaki sannan suka yi awon gaba da shanu da tumakai da awakai da agwagi har ma da abincin da aka adana.
Shugaban al’ummar ta Bokkos ya ce harin na zuwa ne kwanaki biyu da kai irin makamancinsa a al’ummar Ndimar – Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma ta jihar da su kai musu ɗaukin gaggawa tare da ganin an hukunta waɗanda ke far musu.
