Rundunar ‘ƴan sanda a jihar Jigawa ta kama wani matashi da ake zargi da kashe mahaifinsa a safiyar Litinin a garin Sara da ke karamar hukumar Gwaram.
Kakakin rundunar, SP Lawan Shi’isu Adam, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun isa gidan mamacin da misalin karfe bakwai na safe inda suka tarar da shi cikin jini bayan da dansa ya kai masa farmaki.
“Bincike ya nuna cewa wanda ake zargi ya sassara mahaifinsa a kafada sannan ya yanke shi a kirji,” in ji SP Shi’isu.
An garzaya da mamacin zuwa asibitin garin Birnin Kudu, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
SP Shi’isu ya kara da cewa rundunar na ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin wannan mummunan lamari, tare da tabbatar da cewa wanda ake zargi yana tsare a hannunsu.
Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa za su gurfanar da matashin a kotu da zarar an kammala bincike.
Lamarin ya girgiza al’ummar garin Sara, inda mutane da dama ke bayyana alhini da mamaki kan wannan mummunan kisa da ake zargin dan ya aikata wa mahaifinsa.
