
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da yin sojan gona da sunan jami’an tsaro tare da aikata laifuka a Kano, Katsina da Kaduna.
mai magana da yawun rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar a yau Asabar 18 ga Oktoba 2025.
Sanarwar ta bayyana cewa waɗanda ake zargi sun haɗa da Aliyu Abbas mai shekara 35, Sani Iliyasu 47, Ashiru Sule 41, Abubakar Yahaya 45 da Adamu Kalilu 45, inda aka kama su da katin bogi, ankwa, kuɗaɗen CFA 2,500, takardun naira na jabu.
Binciken rundunar ya nuna cewa waɗanda ake zargi sun dade suna amfani da sunan ’yan sanda wajen damfarar jama’a da karɓar kuɗi ba bisa doka ba, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar da cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani nau’i na amfani da sunan jami’an tsaro wajen aikata laifuka ba, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da sanar da duk wani motsi da ba su gamsu da shi ba ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.