
Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai mummunan hari a ofishin ƴansanda na garin Zonkwa a ƙaramar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna, inda suka kashe a ƙalla jami’an biyu da ke bakin aiki.
Harin ya ya auku da yammacin Juma’a wanda hakan ya jefa mazauna garin cikin tsoro da tashin hankali.
Wani ganau da ke kusa da wurin ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun zo ofishin ƴansandan ne ɗauke da makamai, suka buɗe wuta babu kakkautawa wanda hakan ya tsoratar da jama’a da maƙwabta dake wurin.
Ya ce manufarsu ita ce su kuɓutar da wasu da ake zargi da an kawo su ofishin ƴansandan daga garin Kachia.
Sai daga baya suka gane cewa waɗanda suke nema ba sa tsare a ofishin a cewar wani jami’in tsaro da ya tabbatar da faruwar lamarin.