
Ƙungiyoyin agaji a Gaza sun yi gargaɗin rufe wuraren dafa abincin da dubun-dubatar Falaɗinawa suka dogara a kai nan da ‘yan kwanaki masu zuwa saboda matsin lambar Isra’ila
Kasancewar watanni biyu kenan da Isra’ila ta toshe duk wata hanyar shigar da kayan agaji zuwa yankin na Gaza wanda zai janyo mummunar yunwa da ba a taɓa gani ba.
Samy Mahdi na ƙungiyar agaji ta ANIR ya bayyana damuwa kan hakan inda ya ce, a baya su kan dafa shinkafa da nama da nau’in abinci mai gina jiki, amma yanzu babu nama bare kayan lambun da suka shigo da su Gaza.
Manyan jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya sun koka kan abin da suka kira zalunci da azabtar da Falasdinawa.