Ƙungiyar Limaman Najeriya a jiya Alhamis ta gudanar da taron yi wa ƙasar nan addu’o’i a Jihar Kano domin neman taimakon Allah dangane da matsalar tsaro da ke ci gaba da ta’azzara a faɗin ƙasar.
Taron wanda aka gudanar a Masallacin Sheikh Ahmadu Tijjani, ya haɗa limamai, shugabannin addini da ɗimbin mabiya daga sassa daban-daban na jihar, domin roƙon Allah kan ƙalubalen tsaro da na siyasa da Najeriya ke fuskanta.
Da yake yi wa mahalarta taron jawabi, Shugaban Ƙungiyar Limaman Najeriya, Sheikh Muhammad Nasir Adam, ya jaddada muhimmancin tsarkake zuciya da komawa ga Allah a matsayin hanya mafi dacewa ta fuskantar matsalolin ƙasa.
Sheikh Nasir ya bayyana cewa Najeriya tana fama da matsalolin ta’addanci, ’yan fashin daji da sauran barazanar tsaro, yana mai jaddada cewa addu’a ita ce babban makamin da ke hannun al’umma.
Sheikh Nasir ya kuma yi kira ga limamai da mabiya a faɗin ƙasar da su ci gaba da yin addu’o’in neman zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa wannan taron da yanzu aka fara a Kano, za a ci gaba da gudanar da shi a dukkan jihohi 36 na Najeriya.
