Wasu ƴanbindiga ɗauke da muggan makamai sun sace tsohon shugaban Hukumar yi wa Ƙasa Hidima ta kasa NYSC, Manjo Janar Mahrazu Tsiga, mai ritaya.
Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar Katsina, Dakta Nasiru Mu’azu ne ya tabbatar da cewa an sace Manjo Janar Tsiga a garin Tsiga da ke yankin ƙaramar hukumar Kankara ranar Laraba da daddare.
Duk da cewa ƙaramar hukumar Kankara na fama da matsalolin ‘yanbindiga, amma garin Tsiga bai saba fuskantar irin wannan matsala ba.
To amma kwamishinan tsaron ya ce a baya-bayan nan sau uku masu garkuwa da mutane na shiga garin tare da sace mutane.
