Ƙungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta kasa ta dakatar da shirin ta na tsunduma yajin aikin da zata fara gudunar wa a yau litinin, bayan sanya bakin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima.
Likitocin sun yi barazanar fara yajin aikin ne sakamakon rashin biyan buƙatunsu da dama, ciki har da biyan bashi da ƙarin girma da sauran su duk da yarjejeniyar da kungiyar tayi da bangaran gwamnatin tarayya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a baya wata Kotun ma’aikata da ke zama a birnin tarayyar Abuja ta hana ƙungiyar shiga kowanne irin yajin aiki a yau litinin.
Da yake zantawa da manema labarai, shugaban kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta kasa Dakta Mohammad Suleiman, ya bayyana cewa an yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne bayan Mataimakin
Shugaban Ƙasa ya shiga tsakani tare da magance wasu daga cikin buƙatun ƙungiyar.
Ya ƙara da cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa ya nemi ƙarin lokaci domin warware sauran matsalolin, kuma Kwamitin Zartarwa na Ƙasa na ƙungiyar ya amince da wannan roƙon.
