Ƙungiyar agaji ta duniya ICRC, ta sanar da ficewarta daga Jamhuriyar Nijar, bayan shekaru 35 tana gudanar da ayyukan jin ƙai a wannan ƙasa.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da ICRC din ta wallafa a shafinta na yanar gizo.
A ranar Asabar din da ta gabata, yayin wata hira da ya yi a gidan talabijin na kasar, shugaban gwamnatin sojin, Janar Abdulrahman Tiani ya zargi ICRC da hada baki da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.
Sai dai ICRC ta cikin sanarwar da ta fitar, ta musanta wannan zargi da ake mata, inda ta bayyana cewa, tsawon sama da shekaru 30 da ta ɗauka tana gudanar da ayyukan jin ƙai, babu abin da ta fi mayar da hankali illa ceto mutanen da suke ccikin halin ni ‘ya su.
