Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce zai gina gadar da ta karye a garin ‘Yanshana dake karamar hukumar Kumbotso.
Gwamnan ya ce a zaman majalisar zartaswa na ranar Laraba zai amince da yin aikin.
Abba Kabir ya bayyana haka ne yayin zanga-zangar lumana da al’ummar garin ‘Yanshana suka gudanar a gidan gwamnatin Kano ranar Talata.
Haka zalika ya bayar da umarnin a gyara tare da kammala aikin makarantar Sakandiren dake yankin.
Ya ce nan da mako biyu za a samar da sabuwar taransfoma a garin tare da baiwa shugaban karamar hukumar Kumbotso umarnin samar da filin makabarta.
Da yake jawabi daya daga cikin jagororin garin ‘Yanshana ya godewa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, bisa amsa koken su tare da bayar da umarnin magance matsalolin da suka addabi garin.
