Kasar Zambiya ta aika wa Chaina Dala Miliyan 80 kimanin Naira biliyan124 da miliyan 023 da dubu 432 a bisa kusure a lokacin da kasar ke fama da matsin tattalin arziki.
ga kamfanin samar da wutan lantarki na ƙasar da ke Kudancin Afirka a bias kuskure.
Sakataren Baitulmalin ƙasar, Mista Felix Nkulukusa ne ya bayyana faruwar wannan lamari a hirarsa da ‘yan jaridu a birnin Lusaka.
An dai aika kudin ne ta asusun kamfanin samar da wutar lantarkin ƙasar ZESCO.
“ An aika da kusan dala miliyan 80 daga wannan asusu bias kuskure, lamarin da ke kara dagula al’amura a kasar ta Zambiya aka tura ƙudin, wanda hakan babban koma baya ne mai ban takaici a daidai lokacin da muke fama da matsalolin tattalin arziki”. Inji shi
Ƙasar Chinan ce ta gina kamfanin samar da lantarkin a matsayin bashi, amma sai aka fara biyan kudin bias kuskure, yayin da ake ci gabatar da Nazari kan basussukan tsakanin ƙasashen biyu.
A watan Yunin shekarar 2023, Zambiya ta amince da masu ba da lamuni na ƙasashen waje don sake fasalin basussukan da ake bin ƙasar na Dala biliyan 6.3 ciki har da Dala biliyan 4.1 da China ke bin ƙasar, domin duba yiwuwar yafe mata.