Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ba bangaren sharia damar cin gashin-kai domin inganta harkokin shari’a.
Gwamnan ya bayyana haka ne a bikin ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya da Hukumar Karbar Korafe-Korafe Da Yaki Da Cin Hanci ta jiha ta shirya a ranar Talata.
Gwamnatinmu ta ba bangaren sharia cikakkiyar dama saboda daya ce daga cikin rukunan mulki.
“Kuma za mu ci gaba da ba Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Jiha goyon bayan da ya kamata domin dakile yaduwar cin hanci tsakanin jami’ai da sauran al’umma”. Inji shi
Gwamnan ya bukaci hukumar da ta kara kaimi wajen bincike domin gurfanar da dukkan wadanda ake zargi da aikata almundahana.
A jawabin Shugaban hukumar Barista Muhyi Magaji Rimingado, ya nemi hadin kan jami’an tsaro, da dukkan masu ruwa-da- tsaki domin dakile cin hanci da rashawa a tsakanin al’umma.
Hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da suka hada da EFCC da ICPC da hukumomin tsaro da sauran kusoshin gwamnati daga ciki da wajen kasar nan, sun halarci bikin.