
Gwamnatin Najeriya ta sanar cewa za a bai wa mahajjatan ƙasar kuɗin guzirinsu a hannu maimakon amfani da kati ko kuma asusun banki.
Wata sanarwa daga ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ta ce, shi ne ya nema wa mahajjatan sauƙin daga Babban Bankin Najeriya CBN.
Wannan ya biyo bayan bayyana damuwa da mahajjatan suka yi game da tsarin da CBN ya sharɗanta na kowane mahajjaci ya yi amfani da katin banki a matsayin wanda zai iya kawo tarnaƙi ga tsari da aikin gudanar da Hajjin 2025.
Ta ambato kwamashinan tsare-tsare da ayyukan kuɗi na hukumar alhazai, Aliu Abdulrazaq, na cewa hakan zai bai wa mahajjan Najeriya damar kashe kudaden dake hannunsu yayin ibadar a Saudiya