
Sojojin ruwan Isra’ila sun tare ayarin jiragen ruwan na Global Sumud da suka nufi Gaza domin kawo karshen kawanyar da Isra’ila ta yiwa Falasdinawa.
Masu kula da tsarin tafiyar ayarin jiragen ruwa da aka yiwa lakabi da ‘Global Sumud’.
Rahotanni na cewa sojin sun tare jiragen tare yin kutse cikin su a ranar Laraba.
Firaministan Italiya Antonio Tajani ya ce, Isra’ila ta ba shi tabbacin cewa dakarunta ba za su yi amfani da ƙarfi ko tashin hankali a kan jiragen ba, yana mai cewa ya kamata a kai wadanda ke cikin jirgin zuwa tashar jiragen ruwa ta Ashdod ta Isra’ila.
A yayin kutsen sojin Isra’ila cikin daya daga cikin jiragen, an ji sojojin na bayar da umarni ga mutanen cikin jiragen ruwan da su jefar da wayoyinsu na salula a cikin ruwa, watakila gudun kar yadawa duniya abin da ke faruwa.
Celeste Fierro daya daga cikin ‘yan agaji a ayarin jiragen kuma dan siyasa daga kasar Argentina ya ɗauki bidiyon yadda sojojin ruwan na Isra’ila suka tsare ayarin jiragen ruwan.
Ayarin jiragen na dauke da kananan jiragen ruwa 20 da mutane 300 daga kasashe 44 wandan da ya kunshe likitoci da ‘yan jarida da kuma ‘yan fafutuka na kasa da kasa.
Jiragen sun taso daga Basalona ta kasar Spaniya sun ratsa ta kasashen Itali da Grika da kuma Tunisiya a inda wasu jirage 20 dauke da kayan agaji suka hadu da su domin zuwa Gaza da niyyar isa ga Falasdinawas dake fama da matsanacin yunwa.

Wannan shine karo na uku da kungiyoyin agaji na duniya ke kokarin karya kawanyar Isra’ila da ta yiwa Falasdinawa.
A kowanne yunkuri Isara’ila na karya laggon kokarin ta hanyar tare ayarin jiragen da kuma hana su isa Gaza