
Sabon shirin wasan kwaikwayon barkwanci na koyo da koyar da harshen Hausa a Premier radio.
Yau Asabar da dare za a soma nuna wasan kwaikwayo na barkwanci a Facebook da kuma Youtube
Shirin mai suna Jami’ar Firimiya irinsa ne na farko da gidan radiyon ya shirya don bunkasa harshen Hausa ta hanyara koyo da koyar wa amma cikin barkwanci.
Jami’ar Firimaiya makaranta ce ta ilimin manya ta yaki da jahilci a inda dalibanta daga sassa daban-daban na Najeriya suka zo koyon karatu da rubutu da kuma lissafi amma a harshen Hausa.
Cikin daliban da akwai Dan gwari da Dan Yarbawa da Dan Sakkwato da Dan Barno da Dan Kabilar Igbo da Buzu da kuma Dan Kurma a inda kowannensu ke kokarin wuce sa’a a wajen iya harshen.
A mata kuwa da akwai Iya Kewano Banufiya da kuma ‘yar Gayu a ba haushiyar Kano.
Fitattun masu gabatar da shirye-shiryen Hausa na kacicic-kacici a gidajen radiyo, Ahmed Idi Sumaila da Yakubu Jibrin Tumbau sune malaman jamai’ar tare da daya daga cikin jaruman barkwanci na Kannywood Auwalu Musa Solo wanda aka fi sani da Alhaji Rabai, shi ya fito a Malam Komai da ruwanka.
Jami’ar Firimiya shiri ne mai dogon zango na kimanin minti 20, za a rika sa shi ne a dandalin sada zumunta na Facebook da Youtube na gidan radiyon Premier daga ranar Asabar 26 ga watan Afrilu daga karfe 9:00 na dare. za kuma kuma a cigaba da nuna wa a kowanne mako.
Sannan a riga sa shi ga masu sauraro a radiyo a duk ranakun Litinin da misalin karfe 9:00 na dare.
Goggagun marubuta a masana’antar Kannywood ne suka rubuta shirin, ciki har da Habibu Sani da Mustapha Musa Masoyin Baba da Ibrahim B. Lawan da kuma marubuciya Amina Yusuf Ali.
Wanda ya shirya shine shugaban sabon sashen wasan kwaikwayo na tashar Malam Yakubu Liman. Zulyadaini Isa Bello kuma ya bayar da umarni.
Duk a bisa tunani da zaburarwar Malam Abba Dabo wanda ya kuma shi ya dauki nauyin shirin.