”Yan sandan daga gwamnati tarayya ne aka turo su don hana taron zikirin da aka saba yi duk shekara na ‘yan darikar Tijjaniya, a cewar gwamnatin Kano.
Rahotannin na cewa ‘yan sanda sun yiwa filin wasan na Kofar Mata kawanya sun kuma hana shige da fice a hanyar zuwa filin sa’io kadan kafin a soma hallara don gudanra da taron zikirin.
‘An ce jami’an tsaron sun kafa shinge sun kuma hana kowa kusantar filin wasan.
Kokarin wakilin Premier Radio na isa wurin a yammacin yau don ganewa idonsa yadda lamarin yake , ya ci tura a inda jami’an tsaron “suka kwace mi shi waya, suka kuma shake shi|”
Tuni dai gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani kan wannan lamari ta bakin Kwamishinan Yada Labarai Kwamared Abdullahi Wayya.
A wani taro na manema labarai da yayi a fadar sarkin Kano, Kwamishinan yada labarai ya ce, gwamnatin tarayya ba ta isa ta hana gwamnatin jihar Kano gudanar da taro ko wanne iri ba a cikin jiharta.
Tun da farko, Kakakin rundnar ‘yan sandan jihar Abubakar Abdullahi Kiyawa ya bayar da wata sanarwar barazanar tsaro a jihar wanda ya sa rundunar ta dauki matakin hana cunkosan jama’a.
Sanarwar da gwamnatin Kano ta yi watsi da shi a matsayin hujja na hana ta yin taron da sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II zai jagoranta a matsayinsa na Khalifan darikar.
A safiyar Alhamis ne sarki Aminu Ado Bayero ya jagoranci wata tawaga ta ‘yan darikar zuwa Bauchi don gudanara da wani zikirin a can tare da Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
A karo na farko a tarihin sama da shekara 30 da gudanar da zikirin a nan Kano a duk karshen watan Janairu don yiwa kasa addu’a. Wanda wannan karo rikicin sarauta a Kano ya haddasa.
Daruruwan mutane mabiya darikar ke halaratar taron zikirin a kowacce shekara.