Hukumar ta samu nasarar cafke su duk da raunin da suka ji wa ma’aikacin
Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), reshen Jihar Kano, ta cafke wasu mutum biyu, Musa Usman da Buhari Ya’u Bashir, yayin wani samame da aka kai karamar hukumar Bebeji.
Hakan ya bayyana ne a cikin wata sanarwa da Kakakin hukumar reshen Kano, Sadiq Muhammad Maigatari ya fitar a ranar Laraba.
“Lamarin ya faru ne a garin Bebeji yayin da jami’anmu dake shiyyar Kiru suka yi kokarin kama matasan biyu sai daya daga cikinsu mai suna Usman Bashir ya soke shi da dan buda”. Inji shi
Sai dai duk da wannan rauni, ma’aikatan sun samu nasarar cafke matasan.
Sun kuma yi nasarar kama miyagun kwayoyi bayan fafatawa mai tsanani tsakanin jami’an NDLEA da wadanda ake zargi.
Kakakin hukumar ya kuma da kara da cewa, suna tsare da masu laifin biyu kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bisa laifukan da suka hada da fataucin miyagun kwayoyi da kuma kai hari kan jami’in tsaro.
Kwamandan hukumar reshen Kano, Abubakar Idris Ahmad ya yi Allah-wadai da harin, ya kuma tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da aiki ba tare da tsoro ba domin kawar da miyagun kwayoyi daga al’umma.