Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a wani gida a kauyen Zakirai, a Karamar Hukumar Gabasawa inda suka sace wani matashi mai shekaru 20 suka yanke yatsan dan uwansa.
Rahotannin sun nuna cewar lamarin ya faru ne da ranar Asabar da tsakar dare misalin karfe 2:15.
‘Yan bindigar su uku dauke da makamai suka afka gidan Alhaji Yusha’u Ma’aruf ne sun kuma yi awon gaba da wasu kayayyaki masu daraja a gidan sun kuma yanke yatsar hannun hagu na dansa mai shekaru 23, Abubakar Yusha’u, suka sace kuma dan gidan mai shekaru 20, Mohammed Bello Yusha’u.
Wani masanin tsaro mai suna Zagazola Makama shi ya tabbatar da faruwar lamarin a shafinsa na X a ranar Lahadi.
Ya kuma yi kira da jami’an tsaro su kara kokari wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Kokarin wakilinmu na ji daga bakin rundunar ‘yansandan jihar ya ci tura.
