Sabuwar Matatar Man Dangote ta samu Karin tagomashi na cinikkayya da kasarar Kamaru ta hanyar sayar mata da mai.
Matatar Dangote da kamfanin Neptune Oil sun yi hadin gwiwa ta fitar da man fetur daga matatar Dangote zuwa kasar Kamaru.
Hadin gwiwar tsakanin kamfanonin biyu ya jaddada kudirinsu na karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin Najeriya da Kamaru tare da biyan bukatun makamashin da yankin ke bukata.
Shugaban rukunin Dangote Alhaji Aliko Dangote, ya ce hakan ba karmin cigaba bane ga kamfanonin biyu da kuma kasashen biyu.
“Fitar da man fetur zuwa Kamaru, na nuni ne na hangen nesanmu na zama daya domin kai Afirka ga zamo wa yanki mai cin gashin kansa a fannin makamashi.” Inji shi.
Ya kuma ce, da wannan ci gaban, sun aza harsashi inda Afirka za ta rika tace albarkatun nahiyarta domin rarraba su a tsakanin jama’arta.
Matatar ita ce ta farko mai girma a nahiyar Afrika kuma ta Bakwai a duniya.
A lokacin kaddamar da ita a jihar Legas a watan Mayun shekarar 2023, shugabannin kasashe biyar ne na Afrika suka halarta.