
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta cafke wani da ke kokarin safarar miyagun kwayoyi zuwa Turkiyya.
Mutumin mai suna Mbala Dajou Abuba kuma ɗan kasar Angola, mai shekaru 42, ta ama shi ne a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano dauke da kwanson kwanson hodar iblis guda 120.
A cewar kakakin hukumar Femi Babafemi, an kama Abuba lokacin da yake shirin shiga jirgin Egypt Air MS 880 zuwa Istanbul ta hanyar birnin Cairo.
“Bayan an yi masa gwajin jiki, an gano cewa ya haɗiye hodar iblis a cikin cikinsa, wanda daga bisani ya fitar da kwanson hodar iblis guda 120, masu nauyin ki logiram 1.829”. in ji mista Femi
Abuba ya bayyana cewa yana gudanar da kasuwanci a Angola kafin ya tsunduma cikin fataucin miyagun ƙwayoyi.
Hukumar NDLEA ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da yaki da masu safarar miyagun ƙwayoyi domin tabbatar da tsaro da lafiyar al’umma.
