Fitaccen malamin addinin Musulunci a kasarnan, Sheikh Ahmad Mahmud Abubakar Gumi ya ce, ‘yanbindigar da suka addabi kasarnan na samun taimakon makamai ne daga kasashen waje masu karfin fada aji.
Shehun malamin ya fadi hakan ne a tattaunawarsa da BBC a ranar Alhamis.
“Yanzu wadannan yan ta’adda suna da makamai masu girman da ko jami’an tsaron kasarnan basu da su, wannan ya tabbatar da cewa tallafa musu ake”. In ji shi.
Dangane da batun Sulhu da yan bindiga da malamin ya shahara a kai, ya ce, rabon shi da shiga daji domin sulhu tun kafin a ayyana su a matsayin yan ta’adda lokacin shugaba Muhammadu Buhari.
