
Daga Aisha Ibrahim Gwani
Wata mata da ba bayyana ko wacece ba, ta cinna wa kanta wuta a garin Bauchi.
Matar da ake kyautata zaton tana da tabin hankali ta banka wa kanta wuta ne a kofar gidan tsohon Firayi ministan Najeriya, Marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa a garin Bauchi.
Wasu na zargin cewa matar data hallaka kanta ‘yar wani tsohon alkalin kotun shari’a a jihar ce,
Ta Kuma ta zo gidan ne a keke Napep dauke da galan kofar the idan ne a keke Napep ɗauke da galan na man fetur.
Bayan ta tambayi ‘yar Balewa, Hajiya Yelwa Abubakar Balewa, wadda ita ce shugabar hukumar kula da marayu da marasa galihu ta Bauchi (BASOVCA), aka shaida mata ba ta nan. Sai ta zuba man a jikinta ta banka wa kanta wuta a bakin ƙofar gidan.
Rahotannin sun ce an garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), inda likitoci suka yi ƙoƙarin ceton ranta, amma daga bisani ta rasu sakamakon munanar ƙunar da ta yi.
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin. Kakakin rundunar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici ƙwarai.
Ya kuma sanar da cewa kwamishinan ‘yan sanda ya umarci gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin.