
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhininsa game da rasuwar Aliyu Abubakar Getso, gogaggen dan jarida kuma shahararren mai yada labarai.
Gwamnan ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga aikin jarida da ma jihar Kano baki daya.
Hakan na kunshe ne cikin sakon ta’aziyyar da Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Lahadi.
“Marigayi Aliyu Abubakar Getso kwararre ne wanda aikinsa ya taimaka matuka wajen bunkasa aikin jarida, yada labarai da wayar da kan al’umma a jihar da ma sauran jihohi.
Ya kuma shahara da kwarewarsa da rikon amana da kuma jajircewa wajen aikin jarida, wanda hakan ya sa ya samu karramawa daga abokan aikinsa da masu ruwa da tsaki a harkokin yada labarai a fadin Najeriya.” In ji gwamna Yusuf.
Marigayi Aliyu Abubakar Getso ya yi aiki a matsayin edita a gidan rediyon Premier da kuma Freedom. Ya ba da gudummawa sosai a gidan rediyon Vision FM. Sannan ya yi aiki a ma’aikatar yada labarai ta jihar Kano.
Baba Getso dan kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya (NUJ) ne, kuma tsohon Sakatarenta Jiha, ya taka muhimmiyar rawar gani wajen inganta ‘yancin aikin jarida da kwarewa.
Sannan ya asance jagora ga ’yan jarida da yawa, waɗanda suka amfana daga jagorancinsa da hikimarsa, da karimci, in ji sanarwar.
Gwamna Yusuf kuma yi addu’ar Allah ya gafarta kurakuransa, ya saka masa da Aljannatul Firdaus. Ya kuma yi addu’ar Allah ya baiwa ‘yan uwa hakurin jure rashin sa.