Asusun Lura da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ko UNICEF, ya fitar da wata takardar karfafa gwiwa game da muhimmancin manufar yi wa yaran nahiyar Afirka rajistar haihuwa, yana mai bayyana hakan a matsayin muhimmin hakkin yaran nahiyar da ka iya inganta tsaro, da kuma samar da damar kyautata rayuwarsu ta nan gaba.
UNICEF ta fitar da takardar ne a birnin Nairobin Kasar Kenya, albarkacin ranar rajistar ‘yan kasa, da tattara muhimman bayanan jama’a karo na 8, da ake yin bikinta duk shekara a ranar 10 ga watan Agusta.
A cewar asusun, kudurin ci gaba mai dorewa mai lamba 16.9, ya yi kira da a samar da bayanan tantance dukkanin daidaikun jama’a, sai dai kuma a yankin kudu da hamadar Sahara, kusan rabin yara ‘yan kasa da shekaru biyar ba a yi musu rajistar haihuwa ba.
UNICEF ya kara da cewa, ya zuwa yanzu kasashen da suka yi wa sama da kaso 90 bisa dari na yaransu rajistar haihuwa sun hada da Algeria, da Botswana, da Saliyo, yayin da bangaren shiyyoyi kuma, yankin kudancin Afirka ke da kaso 88 bisa dari na yaran da aka yi wa rajista, sai yankin kudancin Afirka mai kaso 63 bisa dari, yayin da yankunan gabashi da tsakiyar Afirka ke da kaso 41 bisa dari.