Sabon Kwamishinan Muhalli ne ya ce, za a biya dukkannin ma’aikatan shara albashin da suke binta bashi
Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli Da Sauyin Yanayi Dakta Dahiru Mohd Hashim a bayyana hakan a ziyarar sa zuwa hukumar kwashe shara ta REMASAB a ranar Talata.
“Zan yi duk mai yiwu wa domin ganin ma’aikatan sharan dake bin gwamnatin hakkokinsu na albashi da alawaus sun samu hakkinsu.
“Tare da fatan hakan zai taimaka wajen su rubanya aikin da suke domin tabbatar da tsaftar muhallan jihar baki daya”. Inji shi.
Gwamnatin za ta yi hakan ne a kokarinta na kara inganta tsaftar muhalli a fadin jihar.
Dangane da hakan ne ya sa gwamnatin za ta samar da abubuwan hawa na musamman da za su dinga aikin debe sharar da al’umma kan tara a unguwannin birnin Kano.
Kwamishinan na ziyartar hukumar ne na gani da ido bayan rantsar da su da aka yi a ranar Litinin.
Manajan Daraktan hukumar Alhaji Lamin Mukhtar ya tarbi kwamishinan.
Ya kuma fadi irin aikin da hukumar ta ke yi na kwashe shara ba dare ba rana da kuma feshin maganin sauron a wasu unguwannin cikin birnin Kano.