
Gawar Matashin kan titi a inda motar ta take mi shi kai
Daga Khalil Ibrahim Yaro
Wani matashi ya rasa ransa, wasu su uku kuma sun tsallake rijiya da baya sakamakon wani mummunan hatsari da ya faru kan titin state road a birnin Kano.

Lamarin ya faru da tsakar rana a dai dai mahadar hanyar zuwa gidan gwamna da titin Audu Bako inda ake bayar da hannu na danja ta Magwan a ranar litinin da misalin karfe 1:00 na rana
Wani matashi mai suna Umar Sulaiman wanda ya shaida lamarin ya ce, tukin ganganci ne da kin bin dokar hanya na direban mota ya haddasa hatsarin.

“Manyan motocin Tifa na dauka kasa na kamfanin aikin titin Gerawa ne guda biyu wanda fitilar bayar da hannu ta tsayar da su, dayar ta tsaya, amma dayar ta ki tsayawa. Rashin tsayawar ya haddasa musu wannan hatsarin”. Inji shi.
Wakilinmu ya raiwato cewa, motar ta buge wanda suke daya gefen ne dake kan mashin a inda daya daga cikin su ya mutu nan take sakamakon take mi shi kai da ta yi sauran kuma suka jikkata.

Gawar mamacin an shimfede shi a tsakiyar titi a ana jiran jami’an tsaro, saura na gefen hanya a jigace alokacin da ya isa wurin.