
Mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ne ya fitar da sanarwar hakan a shafinsa na X a safiyar Laraba .
Shugaban kasa ya kuma maye gurbinsa da Bashir Bayo Ojulari a matsayin sabon shugaban kamfanin.
Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya yi garambawul ga kwamitin gudanarwar NNPC mai mutum 11 ƙarƙashin jagorancin Cif Pius Akinyelure wanda aka naɗa a watan Nuwamba na shekarar 2023.
Haka kuma, sanarwar ta ce an naɗa sabbin mambobin kwamitin gudanarwar NNPC wanda Ahmadu Musa Kida zai jagoranta.
Shugaba Tinubu yana sa rai sabon kwamitin gudanarwar ya ƙara adadin ɗanyen man da NNPC yake tacewa zuwa ganga 200,000 nan da shekarar 2027 sannan ya kai ganga 500,000 zuwa shekarar 2030, in ji sanarwar.
Ana iya tuna cewa dai tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya naɗa Mele Kyari a matsayin shugaban kamfanin na NNPC a shekarar 2019 bayan Maikanti Baru ya yi ritaya.