
Aminu Abdullahi Ibrahim
Kungiyar tabbatar da adalci a sha’anin haraji da shugabanci (Tax Justice & Governance Platform) ta bukaci yin aiki ga al’umma da kudin harajin da suke biya.
Babban jami’in kungiyar Sadiq Muhammad Mustapha, ne ya bayyana haka yayin taron horaswa na kwanaki biyu ga ƙungiyoyi da masu gudanar da sana’o’I domin bayar da shawarwari kan yadda za a samar da manufofi da dokoki da zasu shafi kowane jinsi.
An gudanar da taron wanda The Tax Justice And Governance, Civil Society Legislative Advocacy (CISLAC) da tallafin Christian Aid, suka shirya a ranakun Talata da Laraba a Cibiyar Nazarin Dimokuradiyya ta Aminu Kano (Gidan Mambayya).
Sadiq Muhammad Mustapha, ya ce sun shiyar taron ne don wayar da kan kungiyoyi da masu gudanar da sana’o’I domin fito da hanyoyi da tsare-tsare da zasu tabbatar da cewa harajin da gwamnati ke karba ya shafi kowa da kowa.
Ya kuma ce taron hanya ce da zasu baiwa gwamnati shawara ta yadda za a tsara dokokin haraji wanda zai tabbatar da kowa ya biya kudi yadda ya kamata ba tare da an tsaurara ko cin zarafin kowa ba.
Ya jaddada bukatar kafa tsarin haraji da zai mayar da hankali ga kowane jinsi.
Ya ce binciken da suka gudanar kan yadda haraji yake taba mata da maza a kasuwannin jihar Kano sai da suka samu hadin kan masu karbar haraji na kananan hukumomi da hukumar haraji ta jiha (KIRS) da ‘yan jarida da kungiyoyin ‘yan kasuwa wajen tsara binciken kafin aiwatar da shi.
Ya kara da cewa manufar gudanar da binciken shine domin lalubo hanyoyin da za a magance matsalolin da ake samu na korafe-korafe da yawan karbar haraji a hannun ‘yan kasuwa.
Ya ce hakan zai rage da kushe musu kasuwanci da kuma inganta harajin da ake karba.
Sadiq Muhammad Mustapha, ya ce hukumar haraji ta jihar Kano da Kannan hukumomi suna karbar irin shawarwarin da suke basu kuma suna fito da sabbin tsare-tsare da zasu saukakawa al’umma wajen biyan haraji.
A nasa bangaren babban mai taimakawa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, kan harkokin haraji, Aminu Shu’aibu, ya ce shugaban hukumar haraji na Kano Zaid Abubakar ya fito da sabbin hanyoyi na saukaka karbar haraji musamman ta shafin internet.
Ya ce karbar haraji ya habaka kuma yanzu harajin da ake karba baya zurarewa a jihar Kano, yana mai cewa hukumar ta (KIRS) na fito da tsare-tsare na ilimantarwa da wayar da kai kan haraji da korafin masu biyan haraji.
Da ya ke jawabi jami’in gudanar da bincike a kungiyar (African Center for Tax & Governance) Dakta Tijjani Ahmad, ya ce an gudanar da binciken ne don magance banbanci da samar da dokoki da zasu rinka duba kowa ne bangare na mata da maza wajen biyan haraji.
Ya ce an kuma duba tasirin dokokin da ake da su akan ‘yan kasuwa da masu gudanar da kananan kasuwanci domin samar da daidaito.
Da take jawabi jami’a daga hukumar wayar da kai ta kasa (NOA) reshen Kano, Grace Musa, ta ce da yawan mutane basa biyan haraji saboda rashin samun kayayyakin more rayuwa daga mahukunta.
Ta ce wasu na kafa hujja da cewa basu da asibiti da makaranta da tituna.
Grace Musa, ta kara da cewa tuni hukumar su ta dauki gabaran wayar da kan al’umma musamman mata kan biyan haraji.
