Ta yi watsi da barazanar tsaro da kuma kira da jama’a da isu fito gobe Asabar don yi taron da aka saba yi duk shekera.
Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Abdussalam Gwarzo ya kai ziyara filin Sani Abacha a daren Juma’a a inda ya shiga filin ya kuma bayyana cewa za a yi taron mauludin babu wanda ya isa ya hana.
Kafin ziyarar, Kwamishinan yada labarai Kwamared Abdullahi Wayya ya kira taron manema labarai ya kuma bayyan matsayin gwamnatin jihar da cewa ba za ta yarda gwamnatin tarayya ta hanata rawar gaban hatsi ba a jihar.
Sannan ya yi watsi da sanarwar barazanar tsaro a jihar da hakan zai sa a hana halastacciyar kungiya yin taro na addini da gwamnatin jihar Kano karabar bakuncinsa da aka fakewa da matsalar tsaro.
“Maganar da ake ta yi na yamadidin wani rahoto da aka samu na tsaro, mu a gwamnatin jihar Kano bamu san wannan ba, ba kuma da makamancin wannan, kuma gwamnatin jihar Kano ta kowacce hanya bata je ta kai makamancin wannan rahoton ba na tsoro da rashin zaman lafiya a jihar Kano.
“Saboda haka muna kira ga gwamnatin tarayya da ta yi gaggawar janye wadannan mutane da ta kawo domin zamansu a wajen baraza ne ga tsar, baraza ne ga wannan tsarin da aka shirya da kuma wannan taro mai albaraka, kuma taro da aka shirya domin yin addu’oi, taro ne neman zaman lafiya da cigaban kasa.
“Don haka muna kira ga shugaban kasa da in bai sani ba ya sani cewa gwamnatin kano ba za ta yarda da irin kitimurmuran da mutanensa suke shukawa ba , kuma gwamnatin Kano ba za ta yi ko gezau kan wannan batu ba”. inji kwamishinan.
Masu lura da al’amura na cewa, wannan mataki na gwamnatin tarayya ba zai rasa nasaba da danbarwar sarautar jihar ba, kasancewar Sarki Aminu ya ja wata tawaga ta ‘yan darikar zuwa garin Bauchi domin gudanar wannan mauludi wanda shekara da shekaru a Kano ake yinsa.