Shugaban ƙasar Venezuela, Nicolas Maduro, ya zargi Amurka da abin da ya kira “ƙirƙirar wani sabon yaki” ta hanyar aika manyan dakaru na ruwa zuwa yankin Caribbean.
Maduro ya ce wannan mataki na Amurka wani yunkuri ne na tayar da hankali da kuma neman hambarar da gwamnatinsa, yana mai bayyana shi a matsayin shiri da aka kulla don kawo tashin hankali a yankin.
Sai dai a nasa ɓangaren, ma’aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ta bayyana cewa an tura jiragen yaƙi ne domin ƙarfafa aikin fatattakar masu safarar miyagun ƙwayoyi daga Venezuela.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya taba cewa “babu buƙatar ayyana yaƙi idan za a iya kashe masu fataucin ƙwayoyi kai tsaye,” kalaman da suka ƙara tayar da muhawara a duniya.
A halin da ake ciki, akwai ƙara samun fargaba kan cewa Amurka na iya shirin hambarar da gwamnatin Maduro. Rahotanni sun ce hare-haren da aka kai a yankin sun riga sun hallaka mutum sama da 40, ba tare da an samu hujja mai ƙarfi da ke tabbatar
