
Majalisar dokokin Chadi ta amince da shirin yiwa kundin tsarin mulkin ƙasar garambawul da zai ba wa shugaban ƙasa Mahamat Idriss Deby damar ci gaba da takarar zabe ba tare da adadi ba.
‘Yan majalisu 236 ne suka goyi bayan shirin yayin da guda yaki amincewa da shi daga cikin ƴan majalisu 257 dake majalisar dokokin.
Mahamat ya zama shugaban ƙasa na rikon kwarya a shekarar 2021 sakamakon rasuwar mahaifinsa Idris Deby da ya kwashe shekaru 30 yana mulkar kasar.
Mahamat ya ɗauki alkawarin gudanar da shugabancin rikon kwarya na watanni 18, amma kuma ya tsawaita zuwa shekaru biyu.
Bayan amincewa da sabon kundin tsarin mulki a watan Disambar shekarar 2023, Mahamat mai shekaru 41 ya tsaya takara sannan kuma ya samu nasara a zaben.
Zaben ya zo da ƙalubale inda masu sanya ido na ƙasashen ƙetare suka ce ba shi da sahihanci.
Amincewa da sabuwar dokar zai bai wa Mahamat damar sake takara idan wa’adinsa na shekaru 7 ya ƙare.
A ƙarƙashin kundin mulkin da ake amfani da shi a Chadi, shugaban ƙasa na wa’adin shekaru 5 sau biyu, saboda haka sabuwar dokar zata fara aiki ne bayan zaben da za’ayi a shekarar 2029.
Wakilan wasu jam’iyyun adawa sun fice daga majalisar lokacin kaɗa kuri’ar canza dokokin tsarin mulkin.
Tsohon firayiministan kasar Albert Pahimi Padacke ya aikewa majalisar da wasikar rashin amincewa da tsarin da ya bayyana a matsayin kama karya da ya saɓawa kundin tsarin mulki.