Ma’aikatar harkokin cikin gidan ƙasar ce ta sanar da haka ranar Asabar, inda ta ce an samu nasarar kama mutanen ne bayan samame da haɗin gwiwar jami’an tsaro suka yi daga ranar 17 zuwa 23 ga watan Afrilu.
Ma’aikatar ta ce tuni an tasa ƙeyar mutum 12,866 zuwa ƙasashensu yayin da aka miƙa wasu da suka aikata laifuka daban-daban hannun ofishoshin jakadancin ƙasashensu domin su samu takardu da suka kamata.
A ɗaya gefen, ma’aikatar jarkokin cikin gidan Saudiyyar ta ƙara da cewa mutanen da aka kama a lokacin da suke ƙoƙarin tsallakawa zuwa ƙasar sun kai 1,360 – inda kashi 44 daga cikinsu suka kasance ƴan Yemen, kashi 54 kuma ƴan Habasha sannan kashi biyu daga sauran ƙasashe.
Haka kuma sanarwar da ma’aikatar ta fitar, ta ce an kuma kama mutum 22 da ke da hannu wajen bai wa mutanen matsuguni da kuma ɗaukar su aiki.
