
Daga Khalil Ibrahim Yaro
Premier Radio ta shirya wasan Sallah na Yara cikin murnar bukuwan Sallah.
An gudanar da Bikin ne a Larabar a harabar gidan rediyon a unguwar Nassarawa ta jihar Kano.
A yayin wasanbikin da aka gudanar a dakin Iyayen yara sun bayyana farincikin su kan yadda Premier ta shirya wasan domin murnar bikin sallah.
yayin wasan an gabatar da tambayoyi na kacici-kacici ga yaran, aka kuma bayar da kyautuka ga wadanda suka samu nasara. Cikin abubuwan da aka yi na nishadi.
Wakilinmu ya tattauna da wasu daga cikin wadanda suka halarcin Bikin, sun kuma ce rana ce da yaran su ba za su manta da ita ba.
Sumayya Maradi daya daga cikin iyayen yara waking linmu ya tattaauna da ita.
” Tabbas wannan taro ya kayatar, yarana sun ji dadin wannan taro da kuma yadda premier ta karrama su.” In ji ta.
Malam Yusuf Baita Yusuf daga unguwar Dabai ya bayyana farin cikinsa kamar haka.
“Wasan da aka shiryawa ‘ya ‘yanna ya kayatar da ni kuma ya sa alakata da premier ta kara karfi”. In ji shi.
Wasan ya gudana ne karkashin jagorancin Shugaban sashin Kasuwancin tashar, Malam Yakubu Tumbau da kuma Maimuna Abdullahi daga sashin kasuwanci.
Ya kuma samu halartar mutane da dama da suka hada da iyayen yara da kuma ma’aikatan Premier.