Gidan Radio Premier ya kafa tarihi da samun mabiya Miliyan Daya a lokaci kankanin.
Da tsakar daren Alhamis tashar ta samu wannan adadin cif-cif a shafinta na sada zumunta na Facebook.
Da wannan nasarar tashar ta kafa tarihi a Kano da Kuma arewacin Najeriya la’akari da cewa an kafata ne shekaru hudu da suka wuce.
- UNICEF Ta Jinjinawa Gwamnan Kano A Bisa Kula Da Kananan Yara
- NAPTIP A Kano Ta Kama Mai Tura Mata Aikatau Zuwa Saudiyya
An bude shafin ne a shekarar 2021, shekaru 4 kenan cif.
Masu bibiyar shafukan sada zumunta dai na cewa wannan shine karo na farko da aka kafa irin wannan tarihi na samun masu bibiya miliyan guda cikin shekaru 4 a tsakanin gidajen Rediyon arewa.
Su ma wasu dake bibiyar shafin sun bayyana jin dadinsu da samun wannan nasara.
Tashar ta tanadi wasu shirye-shirye na musamman don murnar cikar wannan matsayi na tarihi.
