
Rahotanni na cewa mazauna garin Uromi da maƙwabta na tserewa daga garuruwansu saboda zaman ɗar-ɗar da fargabar hare-haren ɗaukar fansa da kuma kamun ƴansanda.
Hakan ya biyo bayan kisan wasu mafarauta 16 matafiya ƴan arewacin ƙasar da ƴan sintiri suka yi a Uromin da ke jihar Edo da kuma samun zazzafan martani daga shugabanni da kuma sayuran jama’a da kuma kiraye-kirayen hukunta waɗanda suka yi wannan aika-aika.
BBC ta rawaito cewa, Shaguna sun kasance a rufe, inda wasu bayanai ke nuna cewa wasu mazauna garin na barin wurin saboda tsoron abin da zai faru bayan kisan gillar da ta faru a ranar Alhamis, a hirarsu da Babangida SBJ Yawuri, shugaban matasan arewacin Najeriya mazauna garin Uromi.
“Yayin da da dama daga ƴan asalin garin ke tsoron shiga kasuwar hausawa ‘yan arewacin garin. Saboda ganin abin da suka yi an ɗauki mataki kwakkwara, kasancewar duk irin abin da suke yi wa Bahaushe a baya, ba a taɓa samun ɗaukar mataki kamar irin wannan ba” In ji Babangida.
A ranar Litinin gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya kai ziyara jaje jihar Kano, inda mafarautan suka fito.
Gwamnan ya kuma ya ɗauki alkawarin biyan diyya ga maharban da aka kashe tare da tabbatar da an hukunta masu laifin.
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ba za ta bar maganar ba har sai an hukunta waɗanda ke da hannu a kisan gillar.
Bayanai sun nuna cewa an kama mutum 40 da ake zargin suna da hannu kan al’amarin.