
Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi Ta Kasa NDLEA ta kama wasu mutane da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihohin Kano da Kaduna da kuma Yobe.
Kakakin hukumar Femi Babafemi ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi
“An cafke wata mata da jakar tafiya cike da wasu miyagun kwayoyi, yayin da a jihar Borno aka kama wani matashi da ƙwayoyin tramadol sama da dubu talatin cikin injin mota.
“A Kano kuma an kama mutane biyu da kwayoyin tramadol sama da 30,000 a Gadar Tamburawa dake karamar hukumar Dawakin Kudu.
“Haka kuma, a Kaduna jami’an hukumar sun kwace tabar wiwi mai nauyin kilo 262 daga wani direba a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.” In ji sanarwar.
Hukumar ta ce ana ci gaba da bincike kan wadanda aka kama tare da gabatar da su a gaban kuliya domin huknta su kamar yadda doka ta tanada.