
Hukumar Kula Da Aikin Hajji Ta Kasa NAHCON ta sanar da samu nasarar kammala jigilar maniyatan aikin hajjin bana a fadin tarayyar kasar nan.
Mai magana da yawun hukumar Fatima Sanda Usara ce ta bayyana hakan a lokacin da take zantawa da manema labarai a birnin Madina.
“Yanzu haka akwai maniyata aikin hajjin bana su kimanin dubu arba’in da daya da dari biyar da arba’in da shida a sahu dari da hudu da hukumar ta yi”. In ji ta.
Kakakin ta kuma ce, gabanin fara jigilar maniyatan sai da hukuma ta yi yarjejeniya da kwamfanonin jigilar wanda hakan ne ya sanya aka samu nasarar kammal jigilar a kan lokaci.
Hukumar ta kuma tabbatar da cewa, za ta fara dawo da maniyatan da zarar sun kammala aikin hajjin ba tare da bata lokaci ba.