Karamin Ministan Gidaje Da Raya Karkara, Yusuf Abdullahi Ata ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aikin gina rukunin gidajen gwamnatin tarayya 500 ke tafiya a Kano.
Ministan ya bayyana hakan ne a yayin da ya kai ziyarar gani-da-ido inda ake aikin gina gidajen da ke tafiyar Hawainiya, inji shi.
Ya kuma yi barazanar mika wa ‘yan kwangilar takardar jan kunne a hukumance.
Kasancewar an tsara kammala aikin ne cikin watanni Hudu amma an haura watanni Bakwai aikin bai kammala ba, inji shi.
Rukunin gidajen, kudirin shugaban kasa Bola Tinubu ne na samar da gidaje 20,000 a kowacce shekara a jihohi 13 na kasar nan ciki har da Kano.
Jihar ta samu kaso mai tsoka a tsarin ne a inda za a gina mata gidaje 500, inji Ministan.
Ya kuma ce gwamnatin ta yi hakan ne domin saukaka wa marasa karfi a kasar hanyoyin mallakar muhalli da kuma inganta rayuwarsu.
Ana gina rukunin gidajen ne a garin Lambu da ke Karamar Hukumar Tofa ta jihar, a inda a kashin farko za a gina gidaje 250 a jihar da kuma sauran jihohin da aka zaba.
Ministan wanda ya taba rike mukamin Kakakin Majalisar Dokokin jihar Kano, an nada shi a wannan matsayi ne bayan wani garambawul da Shugaban kasa ya yi wa majalisar ministocinsa.