
Matasa ‘yan Najeriya shida ne suka lashe gasar Hadisi da Gidauniyar Saraki Mohammed na VI ta Malaman Afrika da ke kasar Maroko ta shirya.
Ɗaya daga cikin alkalan gasar Dakta AbdulGaniyu Tijani ne ya bayyana hakan yayin bikin rufe gasar da aka gudanar a birnin Abuja a ranar Asabar.
Waɗanda suka lashe kyautar a rukuni na farko sune Fatima Turbo da Muhammad Ibrahim da Abubakar Abba dukkansu daga jihar Borno.
A rukuni na biyu kuwa, akwai Saleh Al-Amin daga Borno da Ahmed Kolawole daga Kwara da kuma Khalifah Jibril daga Kaduna sune suka fito zakaru.
Kowane rukuni yana da masu nasara uku inda na farko ya samu Naira dubu 250,000, na biyu suka samu Na’urar 200,000, sannan na uku suka samu 150,000 a matsayin kyauta.