
Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta kama wani ango da abokansa 3 bisa zargin kisan amarya a kokarinsu na yin lalata da ita.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Tungo a karamar hukumar Suke Tankarkar a ranar Asabar da dare.
Jaridar Leadership ta rawaito cewa, angon mai suna Auwal Abdulwahab mai shekara 20, tare da wasu abokansa uku; Nura Basiru da Muttaka Lawan da kuma Hamisu Musa sun tilasta amaryarsa yin jima’i da su, a ƙoƙarin tursasa mata ta rasu.
Bayan samun rahoton aikatan laifin, jami’an ‘yan sanda suka garzaya wurin inda suka ɗauki gawar marigayiyar zuwa Asibitin Ƙwararru na Gumel, likitoci suka tabbatar da rasuwarta da isar su.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jigawa SP Lawal Shi’isu Adam ya bayyana cewa, waɗanda ake zargi sun shiga hannu kuma za su fuskanci tuhume-tuhume na haɗin baki da kuma kisan kai.
Haka kuma, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP AT Abdullahi, ya bada umarnin a mika shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ke Dutse domin gudanar da cikakken bincike.