
Kungiyar tuntuba ta dattawan Arewa (ACF) ta yi Allah-wadai da kokarin lalata Masana’antar Man Fetur ta Dangote, tana mai kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kare wannan muhimmin kamfani dake matsayin babban dukiyar ƙasa.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labaran kungiyar Farfesa Tanko Baba ya sanya wa hannu, kungiyar ta bayyana damuwa kan abin da ta kira yunkuri a fili na hana kamfanin ci gaba da aiki yadda ya kamata.
Kungiyar ta kuma ce, tun daga lokacin da aka fara shirin gina matatar har zuwa kaddamar da ita, ta fuskanci ƙalubale da dama, ciki har da wahalar samun danyen mai daga NNPCl da dokoki da kuma ka’idojina da matsalar farashi da kuma tashin hankali daga ƙungiyoyin ma’aikata.
ACF ta zargi ƙungiyoyin ma’aikatan sashen mai na IPMAN da NUPENG da kuma PENGASSAN da yunkurin tilasta wa ma’aikatan kamfanin shiga ƙungiyar, abin da ta ce sabawa ’yancin mutum dan adam ne kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Kungiyar ta jaddada cewa, ko da yake ma’aikata na da ’yancin shiga ƙungiya, amma ya yi a bari masana’antar ta daidaita harkokinta kafin fara aiwatar da irin waɗannan matakai, tana mai goyon bayan ra’ayin Sanata Adams Oshiomhole da Sanata Mohammed Ali Ndume kan batun.